UwarBatoorl96
MADUBI
A wasu lokuta da dama, Buri, Muradi, da Nufi, abubuwa ne mabanbanta da su ke bisa doron hanya ɗaya, domin ana iya ɗaura su a mizani guda, kamar yadda su ke sarƙafe da zare guda ɗaya, wato zaren Ƙaddara. Idan aka ce Ƙaddara ana nufin abinda Allah ya rubuta ya kuma zana zai wanzu a rayuwar bawa tun ma kafun samuwar bawan, abu ne wanda bawa ba ya taɓa kauce masa, haka kuma ba ya taɓa iya guje masa duk tsanani kuwa. Ƙaddara wata kalma ce da ke ɗauke da fuska biyu, tsari biyu, zubi biyu, zane biyu, wato kyakkyawa da kuma kishiyarta.
A zahirin gaskiya, muna saƙa burukanmu ne kawai da kuma muradanmu, haka ma muna nufin wasu lamuranmu ne ba tare da mun duba cewa Ƙaddara ba ta ba da zaɓi ba, tabbas Ƙaddara ba ta bai wa bawa zaɓi, duk da a wasu lokutan Ƙaddara ta kan zo kafaɗa da kafaɗa ne da muradan mu, amma a wasu lokutan shatale ƙafafuwan burukan mu take ba sani ba sabo, wanda hakan ya isa ya shaida wa bawa, wannan kalma ta, "Tun ran gini tun ran zane", wato bawa ba ya tsallakewa Ƙaddararsa.
Sarki ya yi wa Baiwa alƙawarin abinda ke cikinta sai ya mulki MASARAUTAR BAHJA har ma ya kai ga kanzaƙin raɗa wa abun cikin suna tun bai shaƙi iskar duniya ba, sai dai kuwa yayi shuka ne a idon makorwa, da saninsa ko ba da saninsa ba ma ce ba, domin masu haƙiƙanin gadon sarautar sun ce sa ji sa gani ta yadda za a binne tsohuwa da ranta.
To jama'a, ga dai buruka da muradai, amma kuma ba wanda ya san me alƙalamin ƙaddara ta riga da ta zana tun fil'azal.
YARIMA BAHJAT, waye Yarima Bahjat?
Masarautu uku ne, kuma mabanbanta, ɗaya bai yi kamanceceniya da ɗaya ba a ta ko wace fiska, kamar yadda ɗaya ba lallai idan ya na da labarin ɗaya ba, haka zalika a ko wanne masarauta da kalar badaƙala, ta'asa da zunzurutun rikitattun lamura da ke tafiya, waɗanda duk yadda za a ba ka su a taƙaice, ba za ka taɓa fahimta ba sai ka tsunduma cikin labarin gadan-gadan, idan kuwa ka na son banbance zare da abawa yadda ya kamata, to ka tabbatar da ka dangana har i