DielaIbrahim
- MGA BUMASA 1,754
- Mga Parte 45
ƘASAR HAUSA
DAURA
AL'ADARMU, al'ada ta kasance cikakkiyar hanyar rayuwar mutane a karkashin yaran su da maban ban ta al'adu, addinin su, muhallin su da kuma zamantakewar su. Al'ada dai na da matukar muhimmanci musamman ma a cikin yaren mutane, ko wanne yare yana da na shi al'adan da kuma banbanci tsakanin wani yare da wani yaren, a hausan ce al'ada na nufin abin da aka gada daga kaka da kakanni.
Al"ummar hausa dai, al'umma ce dake zaune a arewa maso yammacin tarayyar Najeriya da kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar. a al'adance mutane ne masu matukar hazaka da baiwa iri da kala ta fannin al'adu da kirkire kirkiren abubuwan al'adu.
DAURA jiha ce ta addini kuma ta taka muhimmiyar rawa a fannin gargajiya a arewacin Najeriya, kirarin da aka fi yima ta shine "Daura ta ABDU tushen hausa"
GIDAN DAURA haka kowa yake kiran gidan mu, mafi akasarin mutanen garin suna mana lakabi da Daurawa saboda zumunci da son ƴan uwan junan mu, Sunan ya samo asali ne tun daga kan Kaka da Kakanni kuma suka kafa tarihi mai karfi a cikin zuriyar gidan daura wanda tarihin ya jima yana tasiri a zuciyoyin al'ummar dake gidan.
Kakannin mu su suka kafa wannan zuri'ar sa'annan sun taɓa mulkan garin Daura a zamanin baya kafinnan mulkin ya fita daga hannun su, sai suka kafa nasu ahalin da tambarin sunan gidan wato Gidan Daura.