AishaMaaruf1
Labari ne akan wata Yar kauye da aka sangarta ta, Duk kauyen su ta addabi kowa ba mai iya tsawata mata, tun daga yara, matasa, yan mata, tsoffi, hatta da sarkin garin duk ta addabe su........................
wani matshin saurayi da baze wuce shekara sha takwas ba ya ce"ya ana miki magana kin miyar da mutane yan iska".
kallan Shi tayi Sama da kasa tana gyara dan kwalin ta sai wani murgude murgude take ta ce"ba yan iska ba karuwai da kwartaye na mai da ku ko kuma ka ce yan goguwa ta fada tana murgude baki tare da hararar shi".
Keh ni za kiwa rashin kunya, ganin yanda ya harzuka yasa ta ja da baya tana shirin ko ta kwana, dan ubanki ni zaki zaga, ja da baya ta yi ta tattare zanin ta ta ce" ba dai ubana ba sai dai ubanka mln salisu mai wankin hula".
Toh wallahi ubanki zan ci idan na kama ki, sai na karya kasusuwan ki dan duk dangin ku ba sa'a na.
Wani wawan birki ta ja har tana kokarin faduwa ta ce"kaiiiiiiii! Amman kai mugun makaryaci ne, tsabar raini da rashin ta ido ni zaka kalla kace min duk dangin mu ba sa'an ka, toh ina ka aje aboki balle kuma yaya mugu ehhhhhh!, ko dai abinda ka ke sha ne ya fara dagula maka lissafi, kun san ku samarin zamanin nan ba a raba ku da aaaa, ta fada tana gwada mishi yanda ake shan taba".
Iya kuluwa ya kulu ya dade yana jin irin rashin mutunci da takewa mutane, abin yau yazo kan shi, dutsen dake kusa da shi ya raruma zai Jefe ta da shi tsohon dake tsaye yana kallon su ya ce"kul dan nan kar ka kuskura", bata ko san suna yi ba dan tuni ta yi gaba...................................