Farinciki Stories

Refine by tag:
farinciki
farinciki

6 Stories

  • JUYIN KWAƊO by SalmaAhmadIsah
    SalmaAhmadIsah
    • WpView
      Reads 792
    • WpPart
      Parts 17
    Shin kun taɓa tunanin cewa wata rana rayuwa za ta muku juyi, irin juyin waina a tanda?. Tamkar yanda rayuwar kwaɗo kan yi juyi daga ruwa zuwa ruwan zafi?. Wani hali za ka tsinci kanka a sanda ƙofofin mafita suka kulle gareka, yayin da kake tsaka da buƙatar hanyar kuɓuta? Yaya za ka yi a sanda kake ji da ganin mutuwa na tunkararka a juyin da rayuwa ta maka irin na kwaɗo?. Shin kun taɓa tunanin cewa rayuwa za ta muku juyi irin na kwaɗo?. Daga zamanin da aka haifeku zuwa zamanin kakannin-kakanninku?. Labarin JUYIN KWAƊO. Labari ne a kan matasa uku da rayuwa ta musu juyi irin na kwaɗo. Daga duniyarsu zuwa duniyar da ba su san da wanzuwarta ba sai a labarai. Shin, yaushe za su koma gida? Wani ƙalubale za su fuskanta kafin su koma gida? Shin, za ma su koma gidan?.
  • DIYAH by zeesardaunerh
    zeesardaunerh
    • WpView
      Reads 618
    • WpPart
      Parts 6
    DIYAH Na tashi cikin gata da soyayya,ban rasa komi ba a rayuwata bangaren dukiya ko wani abu na kyale-kyalen rayuwa amma hakan baisa na kasance cikin farin ciki ba. Ada ina rayuwa cikin farinciki da soyayyar Ahali,cikin kankanen lokaci kaddara ta giftawa Rayuwata wacce ta yi sanadiyar rasa farin cikina. Mahaifina ba ya son talaka ,ba ya son ya rab'eshi idan ba lokacin bukatarsu ya yi ba wato lokacin zabe . A ya yin da ni kuma murmushi ya kan samu muhallin zama akan fuskata ne idan na kasance cikin talakawa, ina ganin yadda suke gudanar da rayuwarsu har nakanji ina sha'awar zama cikinsu domin sukan gusar da duk wata damuwata idan ina tare dasu. Narasa abu mafi muhimmaci a rayuwata sanadin wani tsatstsauran ra'ayi na mahaifina sannan na rabu da ahalina sanadin soyayyar talaka wacce tayi kutsen shigowa rayuwata ba tare da shirina ba. kubiyoni domin jin cikakken labarin HALIMATUS-SADIYAH [DIYAH]
  • BOYYAYEN SIRRI A CIKIN SIRRI by NabAbarar
    NabAbarar
    • WpView
      Reads 17
    • WpPart
      Parts 3
    Tausayi, Wahalar Rayuwa , Makirci da kuma Sadaukarwa.
  • WASA FARIN GIRKI(cigaban gidan gandu) by SAKHNA03
    SAKHNA03
    • WpView
      Reads 3,127
    • WpPart
      Parts 1
    Paid book#200 naira ......Me baba yake nufi?,shikenan wai na hakura saina zauna lafiyah a gidan sameer?!! Inaaa hakan bazai taba yi wuwa ba,dan barikin sajojin dayake takama dashi saina maidashi tamkar kango,barekuma gidansa kam sai yayi daya sanin sakani a cikinsa. Domin natsani zama da dawani a rayuwata bare kuma aure.......hmmmm muje zuwa yanzu za'a fara wasan.
  • LABARINSU by SalmaAhmadIsah
    SalmaAhmadIsah
    • WpView
      Reads 1,940
    • WpPart
      Parts 17
    Kowa ya na da Labarin da zai bayar. Kamar yanda ƙaddarar kowa take da ban. Tabbas, akwai tsanani a rayuwa. Akwai ƙunci da baƙin ciki a rayuwa. Shin menene LABARINSU?
  • HASKE by SalmaAhmadIsah
    SalmaAhmadIsah
    • WpView
      Reads 1,029
    • WpPart
      Parts 10
    Akwai wasu ƙaddarorin da kan zo da wani irin duhu, wanda zai mamaye rayuwar ɗan adam, ta yanda ko da tafin hannunsa ba zai iya gani a cikin wannan duhun ba. Kuma an ce HASKE ne kaɗai ke maganin duhu. Ɗan adam kan shiga halin neman HASKEn da zai yi amfani da shi wurin gusar da wannan duhun dake bibiyar rayuwarsa. Shin menene duhun? Wasu tarin ƙaddarori ne waɗannan da ke tafe da matsanancin duhu?. Shin a ina wannan HASKEn yake? Sannan kuma menene wannan HASKEn?