zm-chubado
A tsakanin duniya biyu mabanbanta, ƙaddara ta yi kutse a tsakanin rayuka biyu. Duk a ƙarƙashin kalma ɗaya.
"soyayyah!"
Tunaninta da duk wata nutsuwarta sun karkata ne akan yadda za ta samo masa mafita daga duhun ƙaddarar da ya dabaibaye rayuwarsa ya hanashi saƙat. sai dai a lokacin da take sanya ran cewa komai ya ƙare Yusuf zai koma ƙasarsa ta haihuwa, a wannan ranar tayi realizing cewa ta faɗa a tarkon masifaffiyar ƙaunarsa. Soyayyar mai tsanani ta ke yiwa Yusuf Hateym Al'qasrawi, kyakkyawan Balarabe ma'abocin Addinin musulunci,saɓanin ita da ta kasance KIRISTA wadda ba ta gasgata kaɗaituwa Ubangiji mahalicci ba.
Abu ne mai matiƙar wahala ace Balarabe masani akan addini Musulunci ya amince da soyayyar Ahalul kitabi, duba da yadda suke nuna ƙyama ga duk wata ƙabila wadda ba ta kasance mai tsaftatacciyar nasaba irin ta su ba.
Mutumin da yayi zurfi a so da ƙaunar Matarsa Yumnah Sulaiman El'ghanee,kyakkyawar Balarabiya mai kwarjini da cikakkiyar nasabar da takai a buga misali. Doctor Chioma Nonso Chukuma, ta Fahimci ba za ta iya karawa da Yumnah Sulaiman a zuciyar Yusuf Alqasrawi ba. Amma duk da haka ta lashi takobin sai ta kafa gwamnatinta a zuciyar Ɗan Mutan QASRAH, ko da hakan yana nufin za ta rasa komai da ta mallaka a rayuwarta ne gabaɗaya.
Shin ya akeji idan zuciya ta zaɓi wanda Addini da Al'ada suka banbanta tsakanin ku?
Soyayya ce? Ko masifa?
Ƙaddara ce? Ko kuskure?
Shin Yusuf Alqasrawi zai iya mantawa da matar da ya jima da mallakawa zuciyarsa ya karɓi Chioma a madadinta?
Zainab Muhammad Chubaɗo
08102777485