zm-chubado
Rayuwarsa a lulluɓe ta ke da duhun da ba na dare ba, ba shi da kowa sai mahaifiyarsa wadda ke azabtuwa da tarin jarabobin da ke bibiyarta, cikin ko wani irin gida akwai haske amma a cikin nasu gida babu sai tarin baƙin ciki da ƙuntatuwa.
Ibrahim Wajagal ya zama gangar duhu mai jefa tsoro a zukatan Al'umar Unguwarsu da kewaye, sannan ya zama murɗaɗɗen ɗa mai sanya mahaifiyarsa hawaye!
Soyayya ta zame masa ciwo, ya yin da tausayi ya koma hukunci. Mahaifiyarsa ta rasa zaɓi, a tsakanin ƙauna da fushi wanne zata ɗauka?
addu'a za ta yi ko ƙorafi?
Haƙiƙa tana buƙatar sauƙi da haske a cikin duhun da ya cinye mata ɗa. Duk da cewa wani duhu ba a haskaka shi da fitila, sai da hasken addu'a da haƙuri kaɗai!