Drwamba
ABIN DA AKA SACE
A garin Kwalla, rayuwa ta kasance kamar kowace rayuwa. Mutane suna dariya, suna soyayya, suna aure, suna ibada, suna kasuwanci. Amma babu wanda ya san cewa akwai wata sata da ta fi sata dukkan sata hatsari.
Ba sata ce ta kudi ba.
Ba sata ce ta dukiya ba.
Ba sata ce ta rai ba.
Sata ce da idan aka yi maka ita, za ka ci gaba da rayuwa kamar kowa... amma ba za ka sake zama kai ba.
Bayan rasuwar kakansa, Aminu ya gaji wani tsohon akwatin katako da takarda guda daya a cikinsa. Wannan takardar ta bude masa kofar wani sirri da aka boye tsawon shekaru. Sirrin da zai sa ya fara tambayar kansa ko mutanen da yake gani a kullum su ne hakikanin su, ko kuwa akwai abin da aka kwace musu ba tare da sun sani ba.
Yayin da yake bin sawun wannan sirri, Aminu zai gano cewa akwai mutane da suka rasa tausayi, wasu suka rasa kauna, wasu suka rasa gaskiya, wasu kuma suka rasa tsoron Allah. Duk suna rayuwa, amma wani bangare na rayuwarsu ya bace.
Waye yake satar wadannan halaye?
Me yasa yake yin hakan?
Kuma me zai faru idan ranar da Aminu ya gano abin da aka sace... ta kasance ranar da zai fara neman kansa?
ABIN DA AKA SACE ba labarin tsoro bane kadai, ba labarin sirri bane kadai, kuma ba labarin soyayya bane kadai. Labari ne mai cike da rudani, bincike, tausayi, cin amana, soyayya, darussa, da manyan juyin labari da za su sa ka sake kallon rayuwar mutane da wata sabuwar idanu.
Domin ba duk abin da ake sata ido yake iya gani ba.
Dr wamba ✍️