khadijaaliyuibrahim
ƘWAI BIYU
(Love and Betrayal)
"...ya kasance yana fama da larurar rashin haihuwa wanda yanayin halittar jikin sa ne ya haifar da ita wanda yake da alaƙa da gado, ba wata larura da ya kamu da ita ba.
Ƙwaiƙwayan haihuwar sa lafiyar su ƙalau, sai dai yanayin tsarin halittar jikin sa yana dauke da sinadarin da ake kira HLA (Human Leukocyte Antigen). Likitoci sun tabbatar masa da cewar; ba kowacce mace ce zata iya samar masa da ɗa ba, sai sa'a wato guda ɗaya jal acikin dubunnai.
Hakan ya saka ya baza komar binciken sa a sirri domin samun macen da garkuwar jikin ta tayi daidai da tasa, wadda zata iya haifa masa yaro. Tsawon shekaru shuru, kasancewar sa mai matuƙar son haihuwa, damuwar sa da kwaɗayin sa a kullum ƙara ƙaruwa suke yi.
Bayan tsawon lokaci aka samu mutum huɗu da ƙyar; ɗaya tsohuwa ce shekarun haihuwar ta sun wuce, ɗaya tana ɗauke da cutar HIV kuma ba musulma bace, ɗaya kuma tana da taɓin hankali tana asibitin kula da masu larurar ƙwaƙwalwa.
Sannan ta ƙarshen wadda itace mahaɗin ƙaddarar sa, ta kasance matashiyar budurwa mai kananun shekaru wadda tayi aure tuni da mijin da yafi soyuwa a zuciyar ta fiye da kowa a duniya.
Ya kasancewar kyakkyawa, kuma matashi mai ji da kansa, mai kunya da tsantsani akan dokokin Ubangiji, daɗindaɗawa ya fito daga wata sananniyar zuri'a wadda tayi ƙaurin suna wajen riƙo da addini, sarauta, tarin dukiya, kyau da kuma taƙama, wannan zuri'a ta kasance bar girmamawa a idon duniya.
Aure ya zame masa shinge daga cikar burin sa, sannan kuma ga matsananciyar soyayyar ta data ƙullu a zuciyar sa da yake jin ko da bazata iya samar masa da cikar burin sa ba, zai iya rayuwa da ita a haka...."
Daga nan labarin ƙaddarar su ya fara.