rahmakabir
Ina yin kuka ni kadai nayi na zucci nayi kuma na fili amma duk da haka nasan ba zai yi mini maganin damuwata ba, ji nake kamar ni kadai ce a duniya wacce ta rayu tamkar marainiyar da aka haifo uwar ta ta mutu tun tana tsumma, bansan ya dadin uwa take ba na dai taso cikin shakku da yakinin ni yar riko ce, domin hatta ga yadda na kasance saniyar ware a cikin Kannena na ke kara tabbatar da hasashe na, sai dai nasan KOMAI YAYI FARKO... Kuma ko wace kunyar farko akwai karshen ta, a kullun ina tunanin ko akwai wani kuskuren dana aikata dana samu kaina a halin da nake ciki tare da auren miji irin Umar mai zuciyar rikau da kansa kawai ya sani. #KOMAI YAYI FARKO..