NainarhKd3
Aure ya haɗa zuciyoyi da suka ƙi juna, sirrika suka lullube ƙauna, kishi ya ƙona alaka. MJ da Hibba sun daure a igiyar ƙiyayya, yayin da Reema - matar MJ - ke da wuta a ƙirji da sirrin da ke barazana.
A can, Prince J - yarima a ɓoye daga wata masarauta mai rikici - ya faɗa soyayya da NoorJahan mai fama da lalurar panic disorder, ita ma tana ɓoye wani sirri mai haɗari.
Jaan da Iklimatu sun ƙulla aure mai sanyi, amma Samira - ƙawa kuma makiyarta sannan mata ta farko ga Jaan, wacce ta shirya aure tsakanin mijin nata da ƙawarta Iklimatu- ta rikide zuwa gobara mai ƙoƙarin kona zaman lafiyarsu.
> "Sirri idan ya cika ƙugiya, sai ya rataye mai shi."
MATAR JAHID labari ne da ke yawo tsakanin ƙaddara, kishi, da ɓoyayyun haƙi. Shin soyayya zata tsira daga wuta irin wannan?
#MATAR JAHID
#By Nainarh KD⁂𝒩𝓀𝒹𝓈❦♡
#coming soon