Jeeedorhh Stories

Refine by tag:
jeeedorhh
jeeedorhh

2 Stories

  • KAUTHAR!!  by jeeedorhh
    jeeedorhh
    • WpView
      Reads 9,828
    • WpPart
      Parts 6
    Yadda ya daga kai yana kallonta ne yasa ta shiga taitayinta babu shiri. Ya fara dumfararta gadan-gadan, kamar wanda yake shirin cinyeta danyarta. Duk dauriyarta kasawa tayi, ta fara ja da baya a rikice, idanunta sun fito waje kuru-kuru, dankwalin dake hannunta ta sanya tana kare fuskarta kamar shi zai kwaceta daga hannunshi. Sai daya danganata da bango, ta jita ta lafe a jiki kamar zata shige ciki., Ya duka yana kallon tsakiyar idanunta da wani irin murmushi na gefen baki kwance akan fuskarshi, taji wasu abubuwa masu kama da jan wutar lantarki na yawo a sassan jikinta.... Murmushi ya sake saki, "kina ta babatu da daga murya akan Anty Ummynki Kauthar, sai dai, me yasa dana kalleki nake ji a jikina kamar ba ita kike tayawa kishi ba? Me yasa nake ji kamar.... kishina ne yake cinki? Me yasa nake hango tsabar kishina kwance a cikin idanunki, iye Kauthar? Me yasa??!!!". Ganin yadda take faman zare idanu kamar kazar da aka lakume za a yanka, yasa ya ja da baya, wannan murmushi nashi dake matukar bata mata rai yana kara fadada akan fuskarshi, sai ya juya ya fita daga dakin. Ta sani, kamar yadda ya sani, bashi da sauran ta cewa, don kuwa ya riga ya gama daureta kam da jijiyoyin jikinta! Ta silale a jikin bangon, zuciya na bugu kamar zata fasa kirjinta, ta samu kanta da maimaita tambayarshi a gareta, 'Me yasa? Kuma me yake nufi?!'. ***************** ***Zaku iya samun cikakken labarin a HIKAYA BAKANDAMIYA yanzu***
  • NADIYA! by jeeedorhh
    jeeedorhh
    • WpView
      Reads 6,542
    • WpPart
      Parts 8
    'Ta dan juya kanta cike da mamaki, tace, "Daddynka kuma? wanene shi?" Yace, "Habib Abdullahi Makama?!" cikin sigar tambaya. Jin sunanshi kadai ma sai daya sanya taji bugun zuciyarta ya canza. A duka kwanakin da suka wuce tun bayan daya ajiyeta a kofar gidansu ya wuce, karya take yi tace babu wata rana da zata fito ta koma ga mahaliccinta bata tunano wannan mutumin ba. Abin har ya kusa zame mata jiki, yin tunaninshi a lokacin da taje yin kwanciya barci. Wasu dararen kuwa har da mafarkinshi da tunanin wannan daddadan kamshi nashi, wanda ta lalubo turaren da yake amfani dashi cikin wadanda ya bata, itama ta mayar dashi nata turaren. Yaudarar kanta take, da take cewa wai tuni ta manta da sha'aninshi da kurar data kwasoshi. Ita tasan karya take yiwa kanta. Duk kuma yadda taso abinda ke tukarta a zuciya kada ya bayyana, sai daya bayyana din. Ta rasa fara'ar kirkirowa tayi koda ta yake ce kuwa, haka bugun zuciyarta ya ki saisaituwa duk yadda taso ta saisaita shi kuwa. Ta daure dai da kyar tace, "ok, na ganeshi. Yana ina yanzu?" Ya dan daga kafada, "ban sani ba nima. Kawai dai yace in zauna a wajenki zai dawo ya daukeni." Ita abin ma sai ya girmame mata, mamaki ya hanata motsi. To ita kuma a su wa? Kuma da wane dalili? Da zai dauko danshi ya kai mata?..." To domin sanin dalilin, don me, kuma me yasa? Sai ku biyoni Ni Jeeddah Lawals tare da Nadiya a wannan tafiyar tamu.