Littafanhausa Stories

Refine by tag:
littafanhausa
littafanhausa

4 Stories

  • ANYA BAIWA CE? by AmeeraAdam60
    AmeeraAdam60
    • WpView
      Reads 13,184
    • WpPart
      Parts 11
    Ajiyar zuciya Fulani Maryama ta sauke sannan ta ce masa, " Wace ce yarinyar? Kuma daga wane gurin zata xo? Babu damar dakatar da zuwan nata? Ya za'ay na gane ita ce dan na ɗauki matakin daya dace akanta?? " Boka ya ce, " Daga ni har sauran matsafan duniya babu wanda ya isa ya ja da yarinyar domin ita ɗin FILSIFI ce, abinda muke kira da FILSIFI kuwa aharkar bokan ci, tarraya ko haɗakar shuɗaɗɗun ruhika mabanbanta daga jinsi Mabanbanta, zo ki duba nan " ya ƙarasa faɗa yana buɗe mata wannan jan littafin da ke gefensa. Zanen wasu matasan mata ta gani guda uku sai dai duk cikinsu babu wacce zanen fuskarta ya fito sosai daga ƙasan kowacce anrubuta wani irin gwamammen rubutu, ta farko ya fara nuna mata yace, " Wannan da kike gani ita ce Muhaibish ita ta rayu ne tsawon dubbannin shekarun da suka gabata, Ƴar Sarkin jinsin Fararen Aljanun ƙarƙashin ƙasa ce, tunda take bata taɓa taka doron ƙasa ba " Zaro idanu Fulani Maryama tayi tana mamakin abinda ya faɗa, ta biyu ya nuna mata ya cigaba da cewa, " Wannan kuma sunan ta Kalimsiyat Ƴar sarkin fararen Aljanu ce amma ta nan doron ƙasa itama ta rayu atsawon dubbanin shekaru, acikin wani littafin bincike na karanta cewar ta yi rayuwa ne tun bayan zuwan Annabi Yusuf (A.S) ita kuma tunda ta ke bata taɓa nutsawa ƙarƙashin ƙasa ba a matsayinta na jinsin aljanu, kuma ita Kalimsiyat mace ce mara haƙuri mai faɗan gaske, kuma abinciken da nayi dukkan su biyun kashe su akayi bisa doron zalinci, kuma abinda zai baki mamaki kusan duka ruhinsu guda ne, sai dai banbancin nahiya da zamani. Sai ta Ukun su ita ce aka ce zata xo aƙarshen zamanin nan, sunanta Rayzuta ita ta haɗa dukkan abubuwan da waɗancen suke dashi harma da wanda suka rasa, ƴar baiwa ce me ɗauke da ɓoyayyun al'amura, ita kanta batasan da wannan baiwa tata ba."
  • TUWON MAKAUNIYA by AmeeraAdam60
    AmeeraAdam60
    • WpView
      Reads 23
    • WpPart
      Parts 1
    Kasancewar ta mai bambamcin zubin hallita irin ta 'yan'uwanta mata, ya sa ta zamo saniyar ware a cikin al'ummar da take rayuwa da su. Ba laifinta ba ne, hasali ita ma wayar gari ta yi da samun baƙin al'amuran da suka cunkushe wa rayuwarta. Silar haka ta zama abar ƙyama da Allah wadai, musamman da mutanen yankinta suke ganin ta zame musu gobara daga teku maganinta Allah. Sai dai kuma a ɓangarenta, tana ganin ta zama tamkar tuwon makauniyar da Allah ke kore masa ƙuda, har aci ba ƙuda babu gashi. Labarin Tuwon Makauniya, labarin wata jajirtacciyar mace ce da take rayuwa da hallitar gemu a fuskarta.
  • TAFIYAR MU (Completed) by suwaibamuhammad36
    suwaibamuhammad36
    • WpView
      Reads 27,566
    • WpPart
      Parts 20
    Rayuwar auren masoya biyun na tafiya daidai yanda suka tsara tun farkon fari, kwanciyar hankali da son juna ya kafu a cikin gidansu wanda hakan yasa suka zama abun burgewa ga jama'a da dama har wasu suna fatan ina ma su ne! Suna tsaka da wannan jindaɗin ne rayuwarsu ta canja salo wanda hakan yayi sanadiyyar bankaɗuwar wani tsohon alƙawari mai wuyar cikawa. Ko yaya rayuwar tasu zata ƙaya?
  • CANJIN MUHALLI by suwaibamuhammad36
    suwaibamuhammad36
    • WpView
      Reads 4,463
    • WpPart
      Parts 10
    Ana kiranta Jidda Sufi, ƴar auta ga Governor Sufi Adam. Duk da jindadi haɗe da tsaron da suke dashi a matsayinsu na iyalan Governor bai hana wani mummunar al'amari faruwa da zuriyarsu ba. Cikin son nisanta kanta da mahaifinta wanda take ganin laifinshi ne sanadiyyar rugujewar farin cikinsu yasa Jidda ta ƙaura daga Nigeria zuwa USA domin ƙarisa shekararta ta ƙarshe na secondary school. A wannan sabon muhallin ne Jidda ta haɗu da mutane farar fata wanɗanda wasu daga cikinsu suka ɗauki duniya gurin baza koli. Shin wace irin rayuwa Jidda zata yi a cikin su? Kuma menene zai faru idan tarihi ya nemi maimaita kanshi? Labari ne mai salo na daban akan waɗanda muke karantawa kullum. And it's a FREE BOOK!!! NOTE: May contain some matured contents.