Matarsayyadee01
"Aure rayuwa ce da ake fata ta zama mafarki mai daɗi...
Sai dai ga wasu, mafarkin na rikidewa ya zama mafarkin tsoro da kuka."
Ta shiga gidan aure da zuciya cike da soyayya, tsarkaka da fatan samun nutsuwa.
Amma da ta buɗe ƙofar aure - ta shiga duniyar raɗaɗi, cin mutunci, da azabar shiru.
Duk murmushinta ɓoye ne,
Duk shiru nata kira ne - kiran taimako da ba wanda ke ji.
Wannan ba labari ba ne kawai...
Kukan mata ne da ba su iya faɗi da baki.
UƘUBAR ƊA NAMIJI (Torment of a Man)
Labarin A'eesha - mace da ta yi aure da bege, amma ta rayu da ciwo.