Mutuwa Stories

Refine by tag:
mutuwa
mutuwa

3 Stories

  • AJALI by ayshart647
    ayshart647
    • WpView
      Reads 50
    • WpPart
      Parts 1
    Taken wannan labarin Soyayyar gaskiya, kuma labarin gaskiya da zai tsuma zuciyar makaranci. Allah SWA ya halicci ababen halitta biyu a duk fad'in duniyar nan, walau jinsin aljannu ko kuma na mutane.Haka kuma ya sanya soyayya a tsakanin zukatan juna, Rabuwa a koda yaushe tana iya faruwa ba tare da kwakkwaran dalili ba, wani lokacin soyayya za ta iya kaura tun kafin a je ga batun Mutuwa. Red alert kenan Komai tsananin soyayyar da ka kewa masoyinka dole wata rana za ka wayi duniya d'aya daga cikinku ya koma ga mahaliccinsa. Idan Haka ta faru ba wai yana nufin shi kenan rayuwar mutum ta zo ƙarshe ba, dole ka d'auki dangana, domin ba ka san sirrin da ke tattare da haka ba.
  • JUYIN KWAƊO by SalmaAhmadIsah
    SalmaAhmadIsah
    • WpView
      Reads 807
    • WpPart
      Parts 17
    Shin kun taɓa tunanin cewa wata rana rayuwa za ta muku juyi, irin juyin waina a tanda?. Tamkar yanda rayuwar kwaɗo kan yi juyi daga ruwa zuwa ruwan zafi?. Wani hali za ka tsinci kanka a sanda ƙofofin mafita suka kulle gareka, yayin da kake tsaka da buƙatar hanyar kuɓuta? Yaya za ka yi a sanda kake ji da ganin mutuwa na tunkararka a juyin da rayuwa ta maka irin na kwaɗo?. Shin kun taɓa tunanin cewa rayuwa za ta muku juyi irin na kwaɗo?. Daga zamanin da aka haifeku zuwa zamanin kakannin-kakanninku?. Labarin JUYIN KWAƊO. Labari ne a kan matasa uku da rayuwa ta musu juyi irin na kwaɗo. Daga duniyarsu zuwa duniyar da ba su san da wanzuwarta ba sai a labarai. Shin, yaushe za su koma gida? Wani ƙalubale za su fuskanta kafin su koma gida? Shin, za ma su koma gidan?.
  • DUNIYA by Fatima_writes_
    Fatima_writes_
    • WpView
      Reads 106
    • WpPart
      Parts 3
    A tunanin Shaheed ya dace da samun Shaheeda, mai zai faru lokacin da aka yi wa Shaheeda kisan gilla a daren aurensu? ba a tsaya a haka ba aka doramai laifin kisan. Waye ya kasheta? Shin Shaheed ne ko Mahaifinshi? Me zai faru lokacinda zargi ya kai kan Sa'ad da Sa'adah? Lokacinda bincike ya kai kan Salim da Salima? Ku biyoni a labarin abokai uku:Shaheed ,Salim da Sa'ad da kaddarar da ta hadasu da kawaye uku:Shaheeda ,Salima da Sa'adah. S&S something.