Princessamrah Stories

Refine by tag:
princessamrah
princessamrah

5 Stories

  • MATAR AMEER by PrincessAmrah
    PrincessAmrah
    • WpView
      Reads 39,203
    • WpPart
      Parts 71
    'Ammi ya zan yi da rayuwata? Ya kuke so in yi da zuciyata? Ban taba ba...daidai da rana daya ban taba mafarkin yin rayuwar aure ba tare da Ameer ba. Na roke ku da Allah ku zuba idanuwanku kawai a kaina, ina ji da kun san yadda zuciyata ke tafarfasa a duk lokacin da kuka yi min zancen auren wani wanda ba Ameer ba da tuni kun daina...' Kuka sosai take yi, kukan da ke fitowa tun daga k'asan zuciyarta yana ratsowa tsakanin idanuwanta. 'Na sani akwai zafi da radadi Ameerah, na san miye so, na san gubarshi saboda ni ma na tab'a dandana. Sai dai Ameerah ba za mu zura miki idanuwa ba, shekarunki ashirin da takwas kenan babu aure, kina zaune jiran gawon shanu. Waye ya san inda Ameer yake yanzu? Wa ma yake da tabbacin yana da rai ko babu?'
  • Bakuwar Fuska by PrincessAmrah
    PrincessAmrah
    • WpView
      Reads 41,986
    • WpPart
      Parts 50
    "Babu wata mace da nake son kasancewa da ita bayan ke Boobah. Babu macen da zan iya rayuwar aure koma-bayanki. Ki amince ki share mini hawayena, na yi alkawarin share miki naki hawayen, na baya, na yanzu, da kuma na gaba wanda ba na ma fatansu, zan kokarta yaki da su ta yadda za su nisance ki, ke da hawaye sai dai na farin ciki, da izinin Ubangijin al'arshi mai girma." Cewar Ishraq Sulaiman, hannunshi dafe da zuciyarshi da ke bugawa da sauri.
  • WATA DUNIYA! by PrincessAmrah
    PrincessAmrah
    • WpView
      Reads 4,635
    • WpPart
      Parts 15
    "Ina son ka Amaan. Na dauki alkawarin ci gaba da kula da kai duk rintsi duk wuya. Zan ba ka gata, zan kaunace ka fiye da yadda nake kaunar kaina, sai dai...!" Numfashi ta ja tana furzar da iska daga bakinta, "Sai dai a boye zan so ka, ba na so kowa ya san da zaman ka, kar ka rinka fitowa a kalle min kai, ina gudun kada idanuwa su yawata a kanka, bak'in idon da tsoro da kokarin ture abin da bai zama jinsi a gare shi ba. Ba na son abin da zai karce kyakkywan jikinka, balle ya had'a da zama silar kashe min kai!" Aafiyah 'yar shekara shida zuwa bakwai a duniya ke magana da wani matsakaicin bak'in kumurci, mai jajayen idanuwa, fatar jikinshi kalar k'asa. Macijin sai fasa kai yake, yana fitar da harshensa da mayar da shi, launin idanuwansa sun sauya zuwa jajaye, yana yi yana kad'a kanshi. Shin a wace duniya ce muke? Ina ne za ta kai mu? Ta yaya aka yi yarinya k'arama ke magana da maciji ba tare da tsoro ba? Tabbas kowa ka gani a duniya akwai dalilin wanzuwarsa akwai kuma manufar alakantuwa da zama sila na bayyanarsa. Sai dai silar da ke cikin tafiya WATA DUNIYAR kan iya shafe labaran da aka shekara sittin ana rubuta shi. Ku shigo ciki a yi tare da ku...kar ku bari labarin WATA DUNIYA ya wuce ku.
  • BABBAN GIDA(HUGE MANSION )🏬 by Mamee23
    Mamee23
    • WpView
      Reads 5,881
    • WpPart
      Parts 4
    IS ALL ABOUT FAMILY RESIDING (DWELLING)IN THE BIG MANSION.. KADAN DAGA CIKI👇🏻 (Alhaji aboki nagaji da yarana da matana,am tired of having vision wyt them,ya zanyi😦 Baba nagaji da zaman gidan nan aure nakeso😳 Alhaji let's disunite,just ka sakeni na gaji da xaman gidan ka,gida kamar dajin sambisa🙄 😂😂)
  • HAKKIN UWA by PrincessAmrah
    PrincessAmrah
    • WpView
      Reads 5,247
    • WpPart
      Parts 13
    Wannan labari ne mai tsananin ban tausayi da taba zuciya wanda kuma ya faru da gaske sai dai 'yan gyare-gyare wadanda ba za a rasa ba. Shin kun san girman hakki kuwa? Kun san girma da darajar da uwa take da shi? Kun san babbar tabewa ce ga mai murje darajar uwa? Kun san cewa hakkinta ba zai bar mutum ba? Ku biyo ni don ganin salon wannan labarin.