Sanazdeeyah Stories

Refine by tag:
sanazdeeyah
sanazdeeyah

2 Stories

  • GANGAR DUHU!  by zm-chubado
    zm-chubado
    • WpView
      Reads 399
    • WpPart
      Parts 10
    Rayuwarsa a lulluɓe ta ke da duhun da ba na dare ba, ba shi da kowa sai mahaifiyarsa wadda ke azabtuwa da tarin jarabobin da ke bibiyarta, cikin ko wani irin gida akwai haske amma a cikin nasu gida babu sai tarin baƙin ciki da ƙuntatuwa. Ibrahim Wajagal ya zama gangar duhu mai jefa tsoro a zukatan Al'umar Unguwarsu da kewaye, sannan ya zama murɗaɗɗen ɗa mai sanya mahaifiyarsa hawaye! Soyayya ta zame masa ciwo, ya yin da tausayi ya koma hukunci. Mahaifiyarsa ta rasa zaɓi, a tsakanin ƙauna da fushi wanne zata ɗauka? addu'a za ta yi ko ƙorafi? Haƙiƙa tana buƙatar sauƙi da haske a cikin duhun da ya cinye mata ɗa. Duk da cewa wani duhu ba a haskaka shi da fitila, sai da hasken addu'a da haƙuri kaɗai!
  • MENENE ILLA TA? by zm-chubado
    zm-chubado
    • WpView
      Reads 769
    • WpPart
      Parts 15
    "Idan kina ganin hakan shine dai-dai a zuciyarki to kiyi hakan BINTOU. ni kuma nayi alƙawarin cewa bazan taɓa dakatar dake ba, sai dai kafin ki zartar da hukuncin da kike ƙokarin zartarwa ina so kiyi tunani Akan ƴaƴan dake tsakanina dake...." cewar EDRIS MUHAMMAD KANKIA, ya faɗi hakan yana kallon tsakiyar idanun Bintou a Sanyaye "bana buƙatar komai daga gareka shiyasa ma naƙe so ka sauwaƙe min wannan jarababben Auren naka. kai in banda ƙaddara mai zai sa in haɗa zuriya da kai? In dan ƴaƴan dake tsakankna da kai ne, yasa kake tunanin zan janye ƙudirina akan ka, to kaje na yafe duk wata alaƙa ta jini dake tsakanina da ƴaƴan ka har Abadah Edris....!." cewar FATIMAH HAMZA MAI-GORO, ta gaya masa haka cikin maɗaukakin ɓacin Rai kasa cewa komai yayi illa zuba mata rinannun idanunsa da yayi yana kallon Yanda take huci tamkar macijiya, cikin ƙoƙarin son ya shanye ɓacin Ransa Edris ya saki wani gajeran murmushi wanda ke baiyana ƙunar dake ransa,. batayi Aune ba ya juya ya bar mata gurin ba tareda ko waiwayenta ya ƙarayi ba, Don ya riga ya ƙudurtawa kansa cewar ba zai ƙara waiwayarta ba har Abada, kamar yanda take fatan Samu a tareda shi.........