Истории Saraki

Выбор тегов:
saraki
saraki

Истории 4

  • AKSHAM (the disabled). на Ouummey
    Ouummey
    • WpView
      Прочтений 623
    • WpPart
      Частей 10
    Rayuwa da ƙaddara tamkar dare ne da rana, yayinda dare ya kawo kai muna rayuwa ne da sanin dole gari ze waye Rana tayi, kamar yadda in Rana ta take muna cike da sanin tabbas dare ze yi!. Shin har akwai zafin kaddarar da zata sa uwa ta guji diyar ta? ta yadda har ta ke kyamar a danganta ta gare ta?!. Wace irin rayuwa ce zata kasance ga yarinyar da mahaifin ta ne kawai take jin dadin sa, yayinda tashi daya ya fadi ya mutu? Kaddara ce ta zama silar haduwar su, se dai a tattare da shi yana jin connection me karfi daga zuciyar sa zuwa gare ta, a lokacin da ya fahimci she's fragile yayi kokarin zame mata strength, se dai shin mahaifiyar da ta kasance me sa ido ga dan ta zata bar hakan ya kasance?!. ku dai ku biyo ni, cikin wannan tafiyar me suna a sama wato AKSHAM, ina me tabbatar muku ba zaku yi nadama ba, it's worth it!!!.
  • CIWON ƳA MACE.. на Ouummey
    Ouummey
    • WpView
      Прочтений 3,047
    • WpPart
      Частей 16
    Rayuwa cike take da kaddarori da dama, dan Adam baze ce tayi imani ba kuma Allah ya kyale shi kawai, dan yadda da wannan imanin se Allah ya rubuto series of jarrabawowi din tabbatar da ingancin imanin namu. Se dai san rai da son zuciya na jagorantar dan Adam ga munanan ayyuka, wanda daga karshe suke jinginawa ƙaddara, akwai ƙaddara, amma kuma a boye cikin kaddarar nan akwai jagorancin wasu munanan halaye, son kai, hassada, bakin ciki, da ire iren su. Akwai wani karin magana da Bahaushe ke amafani da shi,musamman a tsakanin mu mata, wanda nake da ja akan shi, da kwarin gwiwa ta, da dukkan zuciya ta, haka da dukkan murya ta nake faɗin CIWON ƳA MACE BE TAƁA ZAMA NA ƳA MACE BA!. Ban yarda da karin maganar wai CIWON ƳA MACE NA ƳA MACE bane, ban kuma aminta ba, shiyasa tun tasowa ta nayi watsi da shi, bangarori da dama da na duba na rayuwar mu mata ya karya ta shi. Ina tunanin bahaushe be fahimci rayuwar mu ba, be karanci mata ba, da na tabbata baze fadi wannan zancen ba balle har ya shiga jadawalin karin maganar mu na Hausa masu tushe da dimbin tarihi. Bari kuji, mace ita ce matsalar mace yar uwar ta, dukkan kukan mace in kun yi duba daga tushe zaku ga daga mace yake, kyashi, bakin ciki, hassada, son kai, munafunci da wasu sauran mugayen halaye da dabi'u sun tare a wajen mata ne. Ba zan ce duka ba dan ko a cikin gidan karuwai akan haifi malami, sedai da yawan mu haka muke, bana tunanin akwai macen da in aka binciki rayuwar ta ba za'a samu tabon yar uwar ta mace ba, in one way or the other, se kuma da na fara fahimtar rayuwa na fahimci DOLE ACE MATA SUN FI YAWA A WUTA.! Ban tsani mace ba dan nima itace, mahaifiya ta ma itace, akwai kuma tarin yayye da kanne, sedai na tsani munanan halayen mu, na kyamaci gurbatattun mata na daga cikin mu, dan sun taka rawar gani cikin KADDARAR RAYUWA TA!. Dan Allah kar ku yanke min hukunci batare da kun saurare ni ba, ina rokon ku ku bani aron lokaci da hankalin ku, ku biyo ni dan jin muguwar rawar da mace ta taka cikin ra
    + еще 9
  • ƳAR DAMFARA на Ouummey
    Ouummey
    • WpView
      Прочтений 1,259
    • WpPart
      Частей 16
    wihuhu 🤸🤸, what came upon your mind seeing this name?! well, I and you know it will be so so so...I can't say!. Just stay tuned and don't miss😍
    + еще 10
  • BA KOWANE SO BANE....... на Ouummey
    Ouummey
    • WpView
      Прочтений 25,922
    • WpPart
      Частей 56
    So da yawa mu yan Adam mu muke tsaurara ƙaddarar mu ta hanyar kin karbar ta kamar dai ni da na kasa karbar kaddarar da Allah yayi min, na butulce masa, na bijirewa iyaye na , na bata da yan uwa na duk akan zabin alkhairi da Ubangiji yayi min wanda na kasa fin karfin zuciya ta in karba nasa kafa nayi shuri da ita. Abinda na manta shine a lokacin da wani ya jefar da abinda yake ganin ba shi da amfani gare shi, a lokacin ne kuma wani zai tsinta ya danke da hannu bibbiyu. Ya so ni da dukkan zuciyar sa, ya kauna ce ni da gaba daya rayuwar sa haka kuma ya bauta min da duk lafiyar sa, amma da me na saka masa?, da mafi munin sakayyar da duk wani dan Adam ze jura. Na wulakanta shi a inda ake ganin darajar sa, na zubar mai da kima a inda ake mutunta shi, kai nayi masa abubuwa da yawan da duk ya jure har zuwa lokacin da ƙaddara ta raba mu ta karfi da yaji wanda na bada gudunmawa ga wannan ƙaddara ba kadan ba. Sedai ba'a dauki lokaci me tsayi ba na gane nice da asara, haka kuma abinda na kwallafa rai din ban samu ba, banda gare gare da kwallon da ƙaddara ta dinga yi da rayuwa ta. A lokacin da ya hakura dani taa dole, ya karbi ƙaddarar rayuwa da zavin Ubangiji gare shi, a lokacin ne wata kaddarar ta sake daure zare me karfi tsakanin mu. Shin da wani ido zan dube shi, da wane karfin halin zan yaki rauni na na karbi kyakkyawar ƙaddara ta?, shin shi ɗin ze bani dama ko kuwa ya rufe babi na? shin har yanzu akwai digon alfarma tsakani na dashi???? #Aimah #Sa'adah #Masdooq #hatred #jealous #depression #destiny all in; #love_story_2024