SalmaAhmadIsah
Shin kun taɓa tunanin cewa wata rana rayuwa za ta muku juyi, irin juyin waina a tanda?. Tamkar yanda rayuwar kwaɗo kan yi juyi daga ruwa zuwa ruwan zafi?.
Wani hali za ka tsinci kanka a sanda ƙofofin mafita suka kulle gareka, yayin da kake tsaka da buƙatar hanyar kuɓuta?
Yaya za ka yi a sanda kake ji da ganin mutuwa na tunkararka a juyin da rayuwa ta maka irin na kwaɗo?.
Shin kun taɓa tunanin cewa rayuwa za ta muku juyi irin na kwaɗo?. Daga zamanin da aka haifeku zuwa zamanin kakannin-kakanninku?.
Labarin JUYIN KWAƊO. Labari ne a kan matasa uku da rayuwa ta musu juyi irin na kwaɗo. Daga duniyarsu zuwa duniyar da ba su san da wanzuwarta ba sai a labarai.
Shin, yaushe za su koma gida?
Wani ƙalubale za su fuskanta kafin su koma gida?
Shin, za ma su koma gidan?.