Hafnancy01
Wani lokaci idan duniya ta rufe maka ƙofa, sai ka rasa a ina za ka samu mafaka. Ƙaddara na iya kai ka wurin da bai kamata ka kasance ba. A cikin wannan labarin wasu matasan mata da rayuwa ta juya musu baya, suka tsinci talatarsu a Laraba sun cusa kansu cikin wani yanayi da ya tilasta musu komawa gadar a matsayin mafakar rayuwarsu. Sun ɗauka cewa gadar za ta zama mafita amma ba su san cewa kowace kyauta tana da farashin ta ba.
Shin wa gadar za ta tsinke da ita? Wace ce kuma zata rasa abin da ta fi so? Wace ce zata tsira daga wannan mummunar ƙaddarar? Kawai ku shirya zance muku domin HARAMTACCIYAR GADA ba labarin da kuka saba ji ba ne. Labari ne da ƙaddara ta haɗa su guri guda, zaɓi, asara da kuma tsira. Kawai ku kasance tare da 'yar mutan Naija Hafnancynku.