zeeyybawa
Tsananin ɓacin rai, tsoro da kuma firgici sune suka taru suka yiwa fuskarta ƙawanya a wannan lokacin da kunnuwanta suka jiyo mata abunda batayi zatonsa ko tsammani ba, da wani irin yanayi mai wuyar Fassaruwa take duban fuskarsa domin sharewa kanta tantamar shin da gaske yake ko wasa, sanin cewa ko mafarki bai taɓa mata makamancin wannan wasan ba sannan kuma fuskarsa bata nuna alamun da wasa yazo ba ya tabbatar mata da cewa abunda yafaɗa daga zuciyarsa ya fito, kawarda kanta gefe tayi domin bazata iya cigaba da kallon fuskarsa wacce take shinfiɗe da zallan zullumin amsar da zata fito daga bakinta ba, iska taja ta furzar ranta sai suya yakeyi tana jin babu daɗi. Daƙyar ta iya sarrafa ƙawazucinta sannan ta daidaita kalaman da suke shirin fitowa daga bakinta wajan ganin batayi amfani da wata dauɗaɗɗiyar kalmar da zata iya raunata jin kimarsa sanin waye shi ba.