We've updated our Content Guidelines.
Review the latest guidelines to keep sharing stories safely.

Zahrasurbajo Stories

Refine by tag:
zahrasurbajo
zahrasurbajo

4 Stories

  • MENENE ILLATA? by zm-chubado
    zm-chubado
    • WpView
      Reads 969
    • WpPart
      Parts 15
    "Idan kina ganin hakan shine dai-dai a zuciyarki to kiyi hakan BINTOU. ni kuma nayi alƙawarin cewa bazan taɓa dakatar dake ba, sai dai kafin ki zartar da hukuncin da kike ƙokarin zartarwa ina so kiyi tunani Akan ƴaƴan dake tsakanina dake...." cewar EDRIS MUHAMMAD KANKIA, ya faɗi hakan yana kallon tsakiyar idanun Bintou a Sanyaye "bana buƙatar komai daga gareka shiyasa ma naƙe so ka sauwaƙe min wannan jarababben Auren naka. kai in banda ƙaddara mai zai sa in haɗa zuriya da kai? In dan ƴaƴan dake tsakankna da kai ne, yasa kake tunanin zan janye ƙudirina akan ka, to kaje na yafe duk wata alaƙa ta jini dake tsakanina da ƴaƴan ka har Abadah Edris....!." cewar FATIMAH HAMZA MAI-GORO, ta gaya masa haka cikin maɗaukakin ɓacin Rai kasa cewa komai yayi illa zuba mata rinannun idanunsa da yayi yana kallon Yanda take huci tamkar macijiya, cikin ƙoƙarin son ya shanye ɓacin Ransa Edris ya saki wani gajeran murmushi wanda ke baiyana ƙunar dake ransa,. batayi Aune ba ya juya ya bar mata gurin ba tareda ko waiwayenta ya ƙarayi ba, Don ya riga ya ƙudurtawa kansa cewar ba zai ƙara waiwayarta ba har Abada, kamar yanda take fatan Samu a tareda shi.........
  • RAYUWAR DIJEE by HUMAIDA224
    HUMAIDA224
    • WpView
      Reads 670
    • WpPart
      Parts 1
    Labari mai cike da tausayi yadda kishiyar uwa a kauye ke kawota asibitin birni ta gudu ta barta a sume
  • MURADIN RAI! by zm-chubado
    zm-chubado
    • WpView
      Reads 5,148
    • WpPart
      Parts 2
    A tsakanin duniya biyu mabanbanta, ƙaddara ta yi kutse a tsakanin rayuka biyu. Duk a ƙarƙashin kalma ɗaya. "soyayyah!" Tunaninta da duk wata nutsuwarta sun karkata ne akan yadda za ta samo masa mafita daga duhun ƙaddarar da ya dabaibaye rayuwarsa ya hanashi saƙat. sai dai a lokacin da take sanya ran cewa komai ya ƙare Yusuf zai koma ƙasarsa ta haihuwa, a wannan ranar tayi realizing cewa ta faɗa a tarkon masifaffiyar ƙaunarsa. Soyayyar mai tsanani ta ke yiwa Yusuf Hateym Al'qasrawi, kyakkyawan Balarabe ma'abocin Addinin musulunci,saɓanin ita da ta kasance KIRISTA wadda ba ta gasgata kaɗaituwa Ubangiji mahalicci ba. Abu ne mai matiƙar wahala ace Balarabe masani akan addini Musulunci ya amince da soyayyar Ahalul kitabi, duba da yadda suke nuna ƙyama ga duk wata ƙabila wadda ba ta kasance mai tsaftatacciyar nasaba irin ta su ba. Mutumin da yayi zurfi a so da ƙaunar Matarsa Yumnah Sulaiman El'ghanee,kyakkyawar Balarabiya mai kwarjini da cikakkiyar nasabar da takai a buga misali. Doctor Chioma Nonso Chukuma, ta Fahimci ba za ta iya karawa da Yumnah Sulaiman a zuciyar Yusuf Alqasrawi ba. Amma duk da haka ta lashi takobin sai ta kafa gwamnatinta a zuciyar Ɗan Mutan QASRAH, ko da hakan yana nufin za ta rasa komai da ta mallaka a rayuwarta ne gabaɗaya. Shin ya akeji idan zuciya ta zaɓi wanda Addini da Al'ada suka banbanta tsakanin ku? Soyayya ce? Ko masifa? Ƙaddara ce? Ko kuskure? Shin Yusuf Alqasrawi zai iya mantawa da matar da ya jima da mallakawa zuciyarsa ya karɓi Chioma a madadinta? Zainab Muhammad Chubaɗo 08102777485
  • SILAR KENAN by zm-chubado
    zm-chubado
    • WpView
      Reads 1,445
    • WpPart
      Parts 1
    Labarin Zuriya