yusuf4797
🔥 BUDURWAR ZUCIYA 🔥
Zuciya ba ta san iyaka ba... amma ƙaddara na iya saka ta cikin zabi mai wahala 💔. Wane ne zai ci nasarar zuciya idan soyayya ta shiga tsakanin jini ɗaya?¿
Zuciya biyu sun haɗu a wuri guda,Soyayya ta haɗu da ƙaddara, Amana ta haɗu da cin amana, A tsakanin uba da ɗa, mace guda ce ta shiga tsakiyar rayuwarsu ba tare da ta san cewa zuwanta zai tayar da wata gobara da za ta sauya komai ba. Wanda ake gani mai gaskiya na iya kasancewa maƙaryaci, Wanda ake gudu saboda tsoro na iya zama mafita. Sai lokacin da sirrin da aka daɗe ana ɓoyewa ya fara bayyana, zuciyoyi suka fara fashewa ɗaya bayan ɗaya. Shin soyayya za ta iya rayuwa idan ta zama tsakanin jini ɗaya? Shin ƙaddara za ta raba su ko kuwa za ta haɗa abin da duniya ta hana?.
"BUDURWAR ZUCIYA"
Labari ne da zai sa ka murmushi, ya sa ka zubar da hawaye, sannan ya hana ka sakat da wayarka har sai ka gano yadda komai zai ƙare in Sha Allah.
#BUDURWAR_ZUCIYA
#Yusuf Adam
#HausaNovel
#LabarinSoyayya