Zulaihat Stories

Refine by tag:
zulaihat
zulaihat

3 Stories

  • MADUBI by SalmaAhmadIsah
    SalmaAhmadIsah
    • WpView
      Reads 28
    • WpPart
      Parts 1
    Koren maciji ne a karkashin koriyar ciyawa. Hauwasa suka ce mugu ɗan masara, ana goyonka kana gemu. An ce da ɗan gari akan ci gari! Shin kun yarda da hakan? Idan ka kalli fuskarka a saman ruwan kogin dake gudana, za ka ji tamkar kana kallon MADUBI ne, domin shi MUDUBI kan bayyanar da zahirin abin da ido ka iya gani... Tunanin nazarin suffarka a saman ruwan zai sa ka ɗauka cewa kai ne da kanka a kan ruwan. Kuma hakan ba shi ke nuna cewa babu wasu abubuwa ɓoyayyu a ƙasan ruwan ba. MADUBI na nuna mana zahirin abin da muka yarda da shi ne, zuciya ita ce ma'ajin sirrin kowani bawa. A nan aka samu tangarɗa! Domin kuwa a duniya babu MADUBIn da zai iya haska zuciyar wani bawa. Da ace za a samu, da sharrika da dama ba su wanzu ba, da ace za a samu, da kullika da yawa sun warware, domin MADUBI ba ya ƙarya, ɗan Adam kaɗai ke yaudarar kansa idan ya so. Ta wani wurin abu guda ɗaya ne ya haɗa su, wato kaddarar mahaifi! A wani ɓangaren kuma abubuwa da dama sun bambantasu, duk da maƙasudin kasancewarsu a halin da suke ciki abu ɗaya ne, hakan ba shike nuna cewa idan suka tsaya suka kalli juna a MADUBI ta ko wani gefe kammaninsu za su zamto ɗaya ba. Rikicin cikin gida, wani babban gida da ya ɓoye tarin sirrika masu ban tsoro, waɗan da idan aka bayyanasu ga mai karatu dole ya jijjiga. Murmushin mutanen dake kewayensa shi ne makaminsu. Mahaifinsu ya tarwatsa rayuwarsu da hannayensa, son zuciya da son kai su ne ke kai mutum ga halaka. Ƙawar dake duniya ita ke ruɗar mutane da dama, sukan yarda da abin da idanuwansu ke gani, ba tare da sanin cewa komai da suke gani gaibu ba ne, duk abin da ka samu, wata rana dole ya ƙare. Abu ɗaya ne da ba zai taɓa sauyawa ba, cewa MADUBI ba ya ƙarya...
  • Zahrah bnt Zannun by Smile-ee
    Smile-ee
    • WpView
      Reads 27
    • WpPart
      Parts 9
    A story of a beautiful muslim decent girl, Zahrah, who has suffered from depression and stress all through her life. Will she be able to over come the unbearable pain she is facing?
  • GIDANMU KOH GIDAN MIJINA by zulaihatmuhammad578
    zulaihatmuhammad578
    • WpView
      Reads 2,545
    • WpPart
      Parts 50
    Pure hatred of a father to his beloved daughter