14 parti Completa Shi ba Makaho bane, amma ido daya gareshi, k'addara ya sa mai nakasu a idonshi na hagu, DANMAKAHO sunan da yan unguwa ke kiranshi dashi.
*
Bata san So ba, daga bisani Allah ya jarabbeta da son dan Shaye-shaye, dan zaman majalisa, dan zaman kashe wando, wanda mutuncin mutum ke zubewa in aka ga kana magana da irinsu.
*
Bata san ya akayi ha, sai tsintar kanta tayi tsundum cikin kogin soyayyarshi. "Me zakiyi da dan shaye-shaye?" Tambayar da kowa ke mata, "ni na san me zanyi dashi, Sonshi nike, Allah ka sa ya aureni, Allah ka sa in zama matar ZAID ALI ZAKI" fatar da ta ke ma kanta cikin zuciyarta kenan.
DAN MAKAHO ZAI CIGABA DA ZUWA MUKU A TASKAR FIKRA KADAI