#6 in Romance 14/04/2017
Tunda take bata taba ganin mugun mutum marar kunya irin Zaid Abdurrahman ba. Ta so ta juya amma ganin su Maami yasa ta fasa ta shigo falon ta gaishe su sama-sama don tare suke da yayanta Saadiq.
Har ma yana tambayarta "Ummu A. da fatan dai wadannan basu baki wahala a wurin aikin?"
Murmushi tayi har sai da kumatunta ya loba sannan tace "Mutanen da suka bini har da roko saboda na musu aiki ba sau daya ba ba sau biyu ba, ai kaga bazasuyi garajen bani wahala ba, don haka ina aikina cikin kwanciyar hankali with full amenities. Ko ba haka ba?" Ta fada cikin dai murmushinta hade da harde hannayenta saman kirjinta.
Idanunsa ya zuba mata tamkar mai karantar duk wani motsi da ruhinta yakeyi, "Saadiq, dole mu kula da Adiyya, saboda ko ba komai ta san yanda take amfani da kwakwalwarta, she's very smart." Ya kare maganarsa cikin murmushi.
Tsumewa tayi hade da aika masa kallon banza, "Dole kace kuna kula da Adiyya, banda dan karan wuyar da kuke bani me kuke yi? kullum nayi aiki sai an kwakulo kuskure a ciki, ko me ya kaishi daukana aikin ma tun farko oho." Barin falon tayi zuwa kicin inda tayi zamanta a can taci abincinta.
Bata sake bi ta kan falon ba bare ta san lokacin tafiyarsa. Tana kwance kan gado sai aikin sake-sake takeyi abu daya ke yawo a kwakwalwarta, kuma hanya dayace da zata bi don magance wannan damuwar- itace ta bar aiki a AZ IT consultants. A karo na uku!
Ko su kadai suke daukan ma'aikatan da suka karanta fagenta ta yafe wannan aikin da irin ukubar da take shiga kullum wayewar gari, "To ma wai aikin dole ne?" Ummu Adiyya ta tambayi kanta, ba tare da sanin dalili ba ta samu kanta tana tsiyayar hawaye. "Duk harda laifin Abba ma yaya za ayi bayan na fada masa komai kuma yace na ci gaba da aiki dasu?"
******