Tafe take tana sanye da riga da siket na atamfa, idanunta na rufuwa a hankali tana kokuwar bud'ewa.
Layi take kamar wacce ta sha kayan maye, hannunta rik'e da cikinta tana yamutsa fuska.
Kayan jikinta yayi bak'i, ya canja launi daga kalar kore zuwa wata kalar daban tsabar daud'a, farat d'aya in aka ce a k'idaya tsawon lokacin da ake sanye da wannan kayan zaka iya d'iba masa shekara da d'ori, sai dai la'akari da yanayin wacce ke sanye da kayan zai sa kayi tunani akasin hakan.
Gashin kanta bud'e yake, k'ura da k'asa turbune ya mamaye ya koma kalar hoda, kitson kanta ya cunkushe ba'a iya ganin tsagunsa.
Siket na jikinta a yage, ana iya ganin farin siketin da ke ciki {under wear} wanda ya koma ruwan k'asa dan datti, ga jirwaye da shatin fitsari da ya mamaye.
"Argghhh!" Ta furta lokaci d'aya ta d'aga k'afarta na dama.