Cikin shagwaba Nabila tace " Umma zaginsa fa yayi yace masa Makaryaci..." Umma ta kalleta da mamaki tace " To ba Makaryacin bane? mutumin da zai bata lokaci ya zauna yana kirkirar labarin da bai faruba ai kuwa babu babban makaryaci kamarsa.." Nabila ta kalli Umma tareda turo baki tace "Umma Nasir d'ina fa ne? Yau har da ke?" Umma tace "lallai yarinya da kin bar maganar wannan Mutumin da baki taba ganinsa ba, kina wahalar da kanki shi baima san kina yiba.." Nabila tace "insha Allahu umma zai san cewa babu wadda ta kaini kaunar sa.." Umma ta tabe baki tace " To wai shi duk iya rubuta labarinsa yakai Abdul Madakin gini ne?" Nabila ta zaro ido tareda cewa "Umma..! ya zaki gama mai rubuta Littafan soyayya da mai rubuta littafan Yaki, ai Nasir dina gwarzone a fagen bada labarin soyayya..."Todos os Direitos Reservados
1 capítulo