Completed on 27th October 2017
#1 in General Fiction more than 10x since 2/10/17,
#2 in General fiction 12/09/17
Afaf ta kasance abar so ga kowa tun daga kakanta har zuwa iyaye da yan uwa har dangi da na nesa, nagartanta da kyawawan dabiu ya haifar mata da wannan soyayya wanda ya zarce har zuwa gidan aurenta in da ta zama mafi soyuwa a wajen uwar mijinta.
Takan raba dare wajen rokon Allah ya azurta ta da miji nagari, cikin rahamar sa ya sada ta da affan a lokacin da batayi zato ba, ya gwada mata soyayyar da ba kasafai ake samu ba, soyayyar da ta ninku zuwa kiyayya yan kwanaki bayan aurensu..