35 parts Complete MatureDaskare wa yayi a wajen tamkar an zare masa rai, sai da yaji wani dumm kamar ba ya duniyar, kafin ya dawo hayyacin sa, wani irin zaro idanu waje yayi ya nufe ta da sauri yana salati
Duƙawa yayi gaban ta, ya saka hannyen sa da kamar za su tsinke tsaban rawan da suke yi, wuƙan ya ɗauka yana me kiran sunan ta
"Ke.. ke ZIYADA.. ke.. tashi mana meye.. haka?" Yayi maganar kamar zuciyar sa zata faso ƙirjin sa tsaban tsoro
Girgiza ta ya hau yi, amma dai kamar ba ta motsi, kamar dai ranta ya daɗe da fice wa a jikin ta.
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. haƙiƙa wannan abun da ya faru ƙaddaran sa ne, mafarin shi ne shigowar ta rayuwan sa, domin ita ɗin ƙaddaran sa ce, kuma Bawa ba ya tsallake wa ƙaddaran sa me kyau ko mara kyau, ABUL KHAIRI ya shiga tsaka me wuya, kuma ya yi dana-sanin bijirewa iyayen sa zaɓin da suka yi masa, ya bi son zuciyar sa.