Attitude miss DEENAH ISMAEEL!! am talking to you right here as a father! Idan da uban ki ne yayi wannan maganar ai babu musu zaki yarda , amma dayake ni kin raina min wayau tunda ba ni na haife ki ba ,shine bari ki nuna min halin ki na y'an duniya ko? Shegiya da ido kamar dattijon biri!!" Uncle Khamis ne ke maganar cikin hasala , daga gani ranshi a b'ace yake. Amma Uncle how can you make such drastic decision without my consent? Maganar aure na fa kuke yi! Kuma hakan ma da mijin da ban tab'a gani ba! That too mai shekaru irin na ubana!" Deenah ta fad'a tana mai d'aga hoton wani dattijo wanda zai yi about 49 yrs ,idanun ta taf da hawaye... Bashida wadda ya tsana duniya irin mace ya tsani a kira mashi mace saboda halin da ya shiga sakamakon yaudaran da mace ta mashi. kwatsam iyayenshi suka neman mashi aure ba yanda zaiyi haka ya aure ta amma da kudurin sai ya muzguna mata ya maidata abun kwatance a gari Mr Imam Sadeeq kenan... Shigowarta rayuwarshi ya ruguza mashi duk wani mugun kudiri da ya d'auka akan mace, ya gane duka mata ba halinsu d'aya ba akwai masu kyawawan halaye...All Rights Reserved