No 1 in General Fiction on 21 September.
A lokaci guda duniya ta yi mata juyi mai zafin gaske. A lokacin rayuwa ta kawo mata zabi mai cike da hatsari da nadama.
Ta yi watsi da duk wata fata, ta dakatar da duk wani mafarki....tun da dama ai mafarki na wadan da suka yi barci ne.
Duk da hakan, Hindu ba ta cire rai ga samun Rahamar Allah (SWT) ba, ko da kuwa zai zo ne a sigar kyakkyawan mutumin da zai kara jijjiga duniyar ta sannan ya dasa kaunar sa cikin zuciyar ta a lokacin da ita kan ta ta yanke kauna ga samun hakan.
Daga ranar da ta amince son sa ya shige ta ta san ba makawa, tun ran gini, ran zane!