Wannan ba labarin mu na gargajiya bane, it's not the normal boy girl thing, wannan tafiya ne wanda zamu kalle duniya ta wani fanni.
Rayuwar da muka tsinci kanmu yanzu bai wuce rayuwa na zalunci ba, masu mulki su tauye ma talakawa hakki, sannan su kuma talakawa suna cikin ukuba babu kwanciyar hankali tareda su. Suna wani irin rayuwa domin su kwata yancin kansu walau hanya mai kyau da kuma mara kyau.
Labarin ya ƙunsa cin hanci da rashawa, sace sace, shaye shaye, safaran mutane da duk wasu mugayen ɗabi'u da bariki ya ƙunsa.