Tana tab'awa kuwa sai taji ta zuuuuuuuuuuu....Gaba ɗayanta hasken yazu k'ota zuwa cikin littafin, ma 'ana ta shige cikin littafin datake kallon hotuna cikinsa. Ga mamakin maryam sai ta ganta ta ɓullo cikin wata sabuwar duniya daban, da irin wacce muke ciki, domin dai inda ta tsinci kanta da ta duba sararin samaniyan-sa saita gansa kore da blue(shuɗi) sharrrr...." wannan wace irin duniya ce kuma" ? Maryam ta duba inda take gaba da baya! Gabas da yamma bataga kowa ba, daga can gefe guda kuma ta hango littafin da take kallo yana nan kamar yanda yake bai canza daga pagin data buɗe ba. "Ikon Allah! taya akayi nazo nan kuma?" lokaci ɗaya tsoro ya ziyarci zuciyarta, Nan take tafara karanto addu'oi a bakinta, bakin nata har rawa yakeyi saboda tsoro da firgico.....
Tafiya tafara zuwa inda littafin yake, ta kai hannu domin ta d'auka, sai littafin ya matsa daga inda yake, tasake kai hannu karo na biyu nan ma littafin yasake matsawa, batareda kuma taga wanda yake taɓa littafin ba, zuwa yanzu
Maryam taji tsoro yayi k'aura daga zuciyarta, dan haka sai ta cigaba dabin littafin, babban burinta shine: tasamu damar rik'e littafin ko da ta hakan Allah zai sa taga hanyar da zata maida ita duniyar data baro.
Ash'nur pyar mera dil.