"Zan dawo miki pretty, Elmansoor is yours, yours alone, banson kukan nan kina karya min zuciya in kinayi, let's be strong, ba'a tab'a samun abu meh kyau sai ansha wahala. Zan tafi in baki sararin yin duk yanda kikeso dan bazan iya ganinki haka ba Aisha, bazan iya jurewa ba".
B'angaren zuciyarsa ya d'aura hannunsa akai ya furta can ciki, muryarsa cike da rauni.
"A nan nake jin duk kukan nan da kikeyi, bana son in mutu ban samu Aisha ba, bana son in tafi ban samu damar kasancewa da farin cikina cikin inuwa guda ba, you mean everything to me, ina sonki fiye da yanda kike zato".