Kamar yadda kowani dan adam ke da buri, Haka itama ta taso da san zama me cinma duk burunkan da ta sa a gaba, sai dai yanayin yadda k'addarata tazo mata, be bata damar cima wasu burunkan nata ba, a lokacin da komai nata ya daidaita , sai ya zamana tana tsakiyar zakarun maza guda biyu da kowanne cikinsu ke mata so na hakik'a, abubuwan sun kacame mata a lokaci da take tunanin bin zabin ranta ta kyale wanda iyayenta suka zaba mata, wanda hakan yayi sanadiyar buduwar wani sirri wanda ita kanta bata san dashi ba
Ku biyoni mu shiga cikin rayuwar ZAHIRAH ABDULRA'UF dan ganin yadda komai ze kaya.
Labarin Zahirah labari ne me cike da tausayi, sadaukarwa, sarkakiya da abubuwan ban mamaki hade wata irin soyayya me cikeda wahalwalu kala-kala.
ZAINABU ABU ta taso a babban gida cikin gata duk da maraicin mahaifiyarta da tayi tun tana yar qanqanuwa. Duk yadda ta so haka take yi a Al'amuran rayuwarta ba tare da shakka ko tsoron komai ba. Salmanu wanda ya zama zabin yayarta da yayanshi ya zama mijinta ba tare da ta amince da hakan ba.