"Wanena halan?" Daya daga cikin 'yan union ya tambaya.
"Alhaji Usman na hwa. Baka gani ZUNNURAIN ga jikin lambar mota nai. Ko da yake duk kuna yaka hwadi ma magana ko yak'i da jahilci baku tai ba." Daya daga cikinsu wanda dagani direba ne yake fadi.
"Allah wadaran naka ya lalace, ashe haka mutuminga yake, ko de cikin hushi yake ne, da azumin rabon abinci yakai kuma duk buda baki ga gidanai 'yan shiyarsu ka buda baki, kwano guda fa, kai 'kila ba shina ba'.
"Shina wulai, Alhaji Usman Gwandu, duk fadin garinga anya da mai arziki nai, gashi zaune cikin talakawa, shekaran jiya ya bude gidan mai nai gazauro wolla inaga sati biyu kenan, duk wanda yibba aiki ba dangi nai na ba, haka yake kwansan matasa zuwa Abuja, Kaduna, Zanhwara, Sokwato yana basu aikinyi. Da yake ma yaransa duk mata ne shi yasa"
"Inji wa? Wolla yana da Da guda, Umair ba kasanga yake ba, ance ko spain ko ina, nima jiya da natai hwadi ma Alhaji mai dakina ta haihu naji suna zantawa ze dawo jibi, wallahi Rago guda da buhun shinkahwa ya aiko min. Allah saka masa da Alkhairi."
"Ameen shi yassa banga laihinsa ba, da ma ya nakada ma shegiya duka muga qaryanta, ita ba arziki ba daga dai ta dan tai boko shike nan tafi qarfin mazan gari.
This story was first published on Facebook and whatsApp 2013, and am publishing it here unedited, so don't mind the errors pls