"kin gama aikin ki don haka ga tukuicin ki". Ya fadi yana sanya hannu cikin aljihunsa yana zaro bandir din yan dubu dubu guda biyu ansa tayi tana mai kau da fuska kamar bata so ba. "Sannan kuma wannan lamarin ya kasance tsakanina da ke in har naji labari mai kama da shigen wannan lamarin kin san Allah sai kin bar filin duniyar nan". Ya karashe fuskarsa a daure kamar bakin hadarin dake kokarin zubda ruwa. Ko a jikin ta bata nuna damuwa da maganganunsa ba illa tsaki da tayi can kasar makoshi ta na balle murfin motar ta fice Khairiyya dake takure bayan mota ta duba da wani irin yanayi na tausayawa tana faman gyaɗa kai kafun ta dubi Alhaji Mati. "batar da sunanka sananne ka aro na banza ka sakawa kan ka akan wani KUDIRI naka na daban...Uhmm ba na ganin wanda ya isa rikakken mutum mara tsoro zai fito da wannan salon na boye sunan sa domin duk wanda yake so ya fado DUNIYAR SHAHARA a wani fanni da sunan sa ya kamata a san shi ko an rufe babin sa ba za taba mantawa dashi ba da abin da ya aikata". Tana gama fadin haka ta buga murfin motar da karfi yan yatsunta biyu ta dagawa Khairiyya wacce a wannan lokacin ta dago da kanta tana dubansu su duka biyun cikin yanayin na rashin inda suka dosa a tsakanin su. "Hajiya Layla" Ya fadi da murmushin mugunta a laɓɓansa kafun ya dora. "...abu daya zai sa na kyale ki a filin duniyar nan shi ne wannan yarinyar da kika bada takomashin taimako har na same ta saboda ita ce hanyar samun arzikina da nake burin cimma wa wannan dalilin zai hanani yi miki komai amma duk da haka ki tsumaye ni ina nan tafe". yatsine fuska tayi kafun ta juya ta fara takawa kan kafafuwanta. Dariya yake yi sosai da sosai har yana buga sitiyarin motar kafun ya tsagaita kamar daukewar ruwan sama fuskar nan tashi ya haɗe ta waje daya kafun yayi wa motar ki ya fizge ta kamar mai kokarin tashi sama.All Rights Reserved