Tun kan in karasa karanta wasikan wata zufa take yankowa daga kowace kofar gashi na jikina.
Da guduwa na shigo dakin Anty shukran ko sallama babu.
Ba in da ban buďe ba daga Bathroom zuwa closet kai hatta karkashin gado na leka babu ita ba alamanta , ina ta dialling no da wayan Mummy da ke hannuna wai switch off. Kan gadon ne , na fada ina fara kuka it can't be true wannan mafarki ne nake yi. Hannuna nasa na dauki Teddy bear da ta ke bala'in so wanda nagani ta bari a kan gadon da kuma bracelet da muka taba sa aka mana an rubuta "Sisters 'forever " na rungumi teddy ďin wani karamin paper ne ya faďo daga jikin " love you my sis