Allah ya sani bata k'aunar zuwa gun matar nan domin daga gidanta zuwa bakin titi inda zata hau napep akwai ɗan tafiya, sai an wuce wasu bishiyoyin dake bayan layin hanyar sam ba tada kyau, idan dai har tayi dare bata cika son biyawa gunta ba saboda tsoro, yau ma dalilin daya ya sata zuwa gidan domin tace mata kuɗi hannu, ita kuma Sadiya indai akwai naira to kukan shirya. Bayan ta baro gidan a yanzu har duhu yayi,tafiya take tana zancen zuci "wannan bishiyoyin Allah ni tsoro suke bani, su suke k'arama hanyar nan duhu fa,amma gari da dan sauran haske, hanya ba haske haka ai sai ama sane ko duka ba wanda ya sani Allah dai ka kaini.,....."
Tana cikin wannan zancen zucin
Ba zato ba tsammani Sadiya taji wani abu ya bugeta gum! Cikin razana tsabar tsoro tayi ihu, dama Sadiya akwai aukin ihu inta ga abin tsoro, Saidai ihun da tayi babu wanda yajiyo ta saboda nisan gun da bakin hanya, tayi yunk'urin juyawa kan ta farga kawai taji kamar anyi sama da ita ta faɗo! Jakarta da ledan magungunan dake hannunta suka zube k'asa daga nan bata k'ara Sanin inda take ba..........Ku biyo mu