"hakika Allah kaine gatana kuma gareka na dogara kai ke kashewa kuma kake rayawa,
kai ke fitar da rayayye a cikin matacce ka kuma fitar da matacce a cikin rayayye. ya Allah ina rokon ka da sunayenka kyawawa da ka barwa kanka sani, da wanda ka barwa Annabawanka sani, da wanda kabarwa Annabi muhhammad SAW sani da kadauke rayuwata idan mutuwata ce Alkhairi a gareni.
ya Allah idan kuwa rayuwata ce alkhairi a gareni ina rok'onka da kasanya DAMUWATA tazamo tarihi a gareni, ya Allah ka kareni da sharrin mashairanta kasanya Aljanna tazamo makomata, hakika ni k'ask'antaciya ce maraya talakar da tarasa gata sai naka ya Allah hakika duk wanda yasamu gatan ka yasamu gatan kowa ya Allah ka k'ara bani hakuri da juriyar rayuwar dana fuskance kaina a cikin ta,