NOT EDITED ⚠️
Yayi kyau matuƙa, yadin ya fito da farinsa da kuma kyaun fuskarsa, Idan ka kalleshi, sai ka ganshi kamar mai cikakkiyar natsuwa da kwanciyar hankali, al-halin sune abubuwan da suka masa tawaye.
A hankali ya sauke ajiyar zuciya yana lasa lip ɗinsa.
Juyowa yayi yana wani taku da idan baka karance shi ba, zaka iya cewa na wulaƙanci ne da nuna isa, al-halin babu hakan a tare da shi ko kaɗan, ƙarasowa yayi gun da Khadijatu take kwance ya duƙo daidai ita, ya hura mata iska a fuska kamin ya kai hannu ya taɓa jikinta.
Hannun yasa ya tallafota ta dawo saman cinyoyinsa, fuskarta na fuskantar tasa, ido ya sakar mata kamar yau ya fara ganinta, a hankali ya kai hannun ya shafa gefen fuskarta, tausayinta ne yake ƙara shiga zuciyarsa.
Shi kansa yana ji a jikinsa akwai wani sirri dake tsakaninsa da haɗuwarsa da Khadijatu, sirrin da har yanzu bai san na minene ba, yana jin shi ɗin wani bangone a shafin rayuwarta, lallai idan har babu shi a ƙaddarar Khadijatu toh babu wanzuwar labarinsa a doron ƙasa, yana ji a jiki da kuma ruhinsa domin ita akayi shi, kamar yadda yake jin da a'ace ya rabu da ita tsakanin jiya zuwa yau da bai san yadda rayuwarsa zata kasance ba, bai san wane irin hali zai samu kansa ba, dan baya taɓa rasa natsuwarsa idan yana kusa da ita, idan tayi nisa dashi ji yake kamar ya rasa wani ɓangare na jikinsa.
Ba sonta yake ba, dan baya tunanin zai iya buɗewa wata ƴa mace zuciyarsa, tun bayan abunda Malak tayi masa, sai dai kuma yana jin fiye da yadda yake ji idan yana tare da Malak, yana jinsa cikin wani yanayi wanda bai taɓa ji ba idan yana tare da Malak.
®
2018