49 parts Complete MatureGuguwar ƙaddara, mai sauya fari ya koma baƙi, haka shima baƙi ya koma fari. Haƙiƙa duk abun da Allah ya ƙaddara zai faru; to dole sai ya faru, kuma Bawa bai isa ya tsallake sa ba
Wata iriyar ƙaddara ce da ta shigo cikin Rayuwar matashin, yayinda tayi tasiri a cikin rayuwarsa har ta canza mishi alƙibla. Zan so ku bi Ni a cikin ƙayataccen labarin nan domin sanin wane ne SHAREEF?
"Wlh ko kukan jini zaka yi SHAREEF sai ka amshi cikin nan a matsayin naka, kana son ka nuna mana bamu san me muke yi ba ne? Kuma yarinyar zata yi maka ƙarya ne? ko kuwa Maryam tana da wayon da har wani zai yi mata ciki sannan ta laƙaba maka ne? To ka canza tunani da dabara, babu yanda za a yi Maryam tayi maka wannan mummunar sharrin, ai dama Likita ya faɗa kana buƙatar Mace a tare da kai, sai ga shi kayi amfani da damar ka ka shiga ka titsiye yarinya ka biya baƙatun ka; sai ya zamana Allah ba azzalumin Bawan sa bane ya nuna maka Iyakan ka, sannan ita ɗin Matarka ce, kai ko ba Matarka bace tunda har ka iya keta mata mutunci dole kai zaka aure ta, tarbiyyar da muka baka kenan ko SHAREEF?" Hhhhh labari mai taɓa zuciya!