KANO Kyakkyawar yarinya ce cikin motar direban ta na tuki, a hankali wanda anata bangare waya ce a hannun ta tana faman latse-latse a dai-dai lokacin ne direban ya yi horn bakin gate din wani katafaren gida. Mai gadin ya yi hanzarin budewa, direban yashiga da motar ciki sosai sannan ya yi parking ya fito hadi da saurin zagayowa ya bude gidan baya ta fito. Yarinyar wacce taci sunan ta Farida za tayi kimanin shekaru shatara zuwa ashirin cif! Kyakkyawa ce a jin farko,ta na da kyawun siffa uwa uba iya tafiya, fannin magana sam-sam ba tada yawan magana, magana ma cewa kake wuyar ta ta ke idan kaga tana wani dan dogon zance, da Dad din ta take Magana ko kuma Mom din ta, sai dai tafi yawan Magana da Yayan ta. Haka ko a cikin mutane take yana da wuya kaji maganar ta, tun kawayen ta na darnuwa har suka yi sabo da halin ta, idan ana Magana cikin kawaye sai idan anyi maganar da zata bada dariya, ko shi din iya kacin ta murmushi. Read More @ www.share4world.com.ng