Ka da sunan ya sa ku yi tsammanin zallar soyayya za ku samu a ciki.
Ka da sunan ya ba ku wani tabbaci na ba zai taba zuciyoyinmu ni da ku ba.
Sunan wani jigo ne, na yadda kaddara ta hau kan rayuwar malabartan, ta yi shimfidarta ta kwanta ba tare da sanin ranar da za ta kama gabanta ba.
Labarin zai dora zuciyoyinmu a wani tsauni mai mugun tsawo. Wanda za mu hau tare da ni da ku da malabartan mu fado, mu ji mu na son mu kara komawa, dan ganin yadda labarin zai warware kanshi.
GURBIN SO... a fiction based on a true life event.
Lubbatu Maitafsir.