Rayuwar matasa
Sharhi:- Wannan littafi nawa ƙiƙirarre ne, kashi ashirin cikin ɗari, ko ma ince bai kai ba shine gaskiya, kuma akansa na ƙirƙiri labarina.
Mas'alar da na ɗauko a yau mas'ala ce mai girma, hakan yasa na ƙirƙiri duk wani SUNAN da na gina labarin a kai, kamar sunan makaranta, sunan kamfani da ma sunayen jaruman littafin. (Note, SUNA kawai, dan duk wani abunda ya samu jaruman littafin, zai iya samuna, ya sameka/ki idan har halin mu yazo iri ɗaya da na su)
Mas'ala ce wanda dole wurin isarwa sai ka yi takatsantsan wurin zaɓen kalmomi, hakan ya sa na ke ɗaukan kowacce kalma da na ajje da muhimmanci, gudun samun akasi, wurin neman gyara a samu ɓaraka.
Ina fata ku fahimceni, kuma ku bi ni cikin haƙuri har zuwa inda zan ajiye alƙalamina, ban ce kada a dawo dani in na kauce ba, hukunci nake son ku ajje gefe guda, har in samu damar isar da nufina.
Idan labarina ya yi shige da rayuwarki/ka, akasi aka samu, ban gina labarina ba sai da na samu cikakken haɗin kai daga wurin wacce ta bani wannan 20% ɗin da na ambata a baya.
Nagode, a sha karatu lafiya!