𝐖𝐀𝐘𝐄 𝐒𝐇𝐈?(𝐒𝐡𝐚𝐟𝐟𝐢𝐪 ko 𝐀𝐡𝐦𝐚𝐝)
40 parts Complete Wasu hawaye taji sun zubo mata, ta fashe da kuka, kukan ta ne yasa hankalin sa ya dawo jikin sa...
Ta hau dukan kirjin sa tana wannan wane irin mugun wasa ne Ahmad, ni bana son irin wannan wasan , kai da bakin ka kace kaima kasan ina sonka...
Dukansa takeyi tana kuka....shidai yayi lamo yana saurarar ta kawai dan bai san hawa ba bare sauka...
Wannan ai ganganci ne akan me zakayi kokarin kashe kanka bayan ni kai ka hana ni kashe kaina...
Idan ban so ka ba wa zan so a duiyar nan ahmad, wa nake da shi bayan kai...
Kaima kasan na dade da kamuwa da sonka, dan allah ka tashi, AHMAD!! AHMAD!! AHMAD!!.....