'Kwallina!'
Zuciyarta ta buga da wannan kalmar, jan jikinta ta fara yi tana son isa inda ta jefar da kwallin, ji take shi kaɗai ne
Zai iya taimakonta, shi kaɗai ne zai iya hana HAMOUD aikata duk wani abu da yake hari.
Dafe kwalbar kwallin ta yi tana ƙoƙarin ɗauka. Da shi da gabjejen takalmin ƙafarsa ya ɗora a hannun nata, ya murje, ya muttsike, ya ƙara murjewa har sai da sautin rugurgujewar kwalbar da yatsunta ya fita, ta kwalla gigitacciyar ƙara jin kwalaben sun lume a tafin hannunta, a haka ta ji sautinsa yana faɗa mata abin da ya dakatar da fitar numfashinta.
"Idan akwai halittar da ba zan taɓa yafewa a duka duniyata ta ba, to ke ce Fakriyya. Ki yi zina da mahaifina, ki keta alfarmar mahaifiyata, ki zo kuma ki aure Ni? Wane irin kwamcala ce wannan? Ki faɗa mini me na miki a rayuwa da za ki min wannan hukuncin? Ta ya ya ma na aure ki, me ya sa na so ki? Me zan miki?...
Lura:
(Akwai tarin sarƙaƙiya a labarin, ku taho a sannu, kuna kiyaye duk wani motsi na jaruman)