Rayuwarta, farincikinta, damuwarta, tashin hankalinta, komi nata ya ta'allaka ga mutanen nan su biyu ne kacal! Su kadai take kallo taci gaba da rayuwa kamar babu wata damuwa a ranta, her world revolves around them!!
Me zai faru lokacin da abubuwa suka canza? Lokacin da tsohon aboki, kuma masoyi ya bayyana a cikin Rayuwarta? Lokacin da 6ataccen Yaya kuma 'Dan uwa Mafi soyuwa a rayuwar ta ya bayyana? Lokacin da bata yi zato ko tsammani ba?? Musamman idan abin yazo da wani zabi da zata yi, zabi wanda yake mai matukar tsanani da wahala...
Shin, ko yaya zata kasance???
☆*☆*☆*☆*☆*☆*☆*☆*
Tafe suke cikin super market din a hankali. Shi yake tura akwatun sayayyar, yayin da Ramlah take makale dashi tana jidar abinda take bukata tana jefawa cikin akwatun.
Dai-dai lokacin data kai hannu kan kwalin 'sponge cookies' tana kokarin dauka, taji hannu ya kamo hannunta ana kokarin daukar kwalin cookies din. Cikin sauri, kuma a lokaci guda, suka saki kwalin ya fadi kasa.
Kamar hadin baki, su duka ukun suka durkusa tare da kai hannun su ga kwalin. Mistakenly, hannun shi ya sauka akan bayan hannunta. Wani hargitsattsen shock da matsananciyar faduwar gaba ya ratsa su a lokaci guda.
Kyawawan dara-dara, kuma fararen idanuwa suka dago suka sauka akan zagayayyiyar, doguwar fuskarta, kafin ya dire su akan wasu irin deep-ocean blue eyes da Idanuwan shi basu taba katarin cin karo dasu ba!
Ya samu kan shi da nutsewa cikin kogon su, yana karantar ta, yana ji a jikin shi, kamar.., kamar...!
Ta kasa janye nata idanun daga cikin nashi, duk kuwa da amsa kuwwar da zuciyarta take mata akan tayi hakan, ta kasa! Kamar wadda maganad'isu ke fuzgar ta, haka take ji. Ita ta sani, kamar yadda zuciyarta ta fita sani, cewa shine!!
Basu samu damar janye idanuwan su akan na juna ba, sai da siririyar muryar karamar yarinyar ta ratsa cikin dodon kunnuwan su;
"Mom?!".
~~~~Wannan littafi sample ne kawai ch (1-24). Zaku iya samun sauran a Taskar Fikra.