WANNENE YAFI FALALA? *"Tsakanin Yin karatun alqurani ko yin azkar bayan Sallar Assuba??"* Shike Abdil'aziz bn Baz Allah yayi Masa Rahama yana cewa: "Zikiran da Addu'oin da aka ruwaito daga Annabi SAW yana yinsu safiya da yammaci,wadanda akayinsu bayan Sallar Assuba da bayan sallar La'asar,yin su a wadan nan lokutan sunfi karatun alqurani,domin abinda ya tabbata Annabi SAW yakeyi awannan lokacin shine azkar da Addu'i ba Karatun Alqurani ba Sannan yin Azkar a wannan lokaci itace ibadar da aka ruwaito ayi awannan lokacin,sabanin karatun alqurani anayinsa ne akowane lokaci. @ﻣﺠﻤﻮﻉ ﻓﺘﺎﻭﻯ ﺍﺑﻦ ﺑﺎﺯ Kuma Annabi SAW yana cewa: *(Na zauna tare da mutane muna ambaton Allah tun daga bayan Sallar assuba har rana ta fito shi yafi soyuwa agareni fiye da in yanta yuyaye guda hudu na ya"yan Annabi Isma'il....)* @ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ، ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ، ٢ / ٦٩٨ Sannan awani Hadisin Yana cewa: *(Duk wanda ya zauna yana ambaton Allah tun bayan Sallar asuba har rana ta fito sannan ya tashi yayi Sallah raka'a biyu,za'a rubuta masa ladar aikin Hajji da Umara cikakku)* @Saheehul Jami'i Allah ne mafi sani. *Allah ka bamu ikon koyi da Aiyikan Annbi SAW alokutan da ya dace*