12 chapitres Terminé Gefen wasu samari uku da suke ta faman tada hayaki kamar tashin duniya ta rakube, ta mikawa Bangis -mai shagon- kudin hannunta.
Tace, "magi mai tauraro zaka bani na talatin da aji-no-moto na ashirin".
Ya zuba mata a leda fara ya mika mata. Ta juya, wani daga cikin matasan ya fesar da hayakin daya busa, ya sauka akan fuskarta. Ta sanya hannu tana kore hayakin, tana tarin daya sarketa sakamakon shakar tabar da tayi har cikin makoshinta.
Ta bude idanunta dake mata zafi, babu mamaki ma sunyi ja, ta saukesu akan wanda ya aikata mata wannan ta'addanci.
Babu abinda ya dauki hankalinta a tattare dashi sai idanunshi, irin idanun dake nuna wuya da tsananin duhun rayuwa da suka gani, suka kuma jure. Duk rashin kunyar mutum, karya yake yace zai tsaga tsakiyar idanun mutumin nan yace zai mishi rashin kunya. Don haka ne yasa ta kame bakinta, 'yar Allah Ya isa din data dauko daga cikinta zata yi, ta tsaya a makoshinta. Ta sadda kai ta kara rabawa ta gefensu ta wuce.
Bata sani ba, wani abu game da wannan bakon mutumi da bata taba gani ba, seems nagging. Ta kasa fitar dashi daga cikin ranta. Dai-dai zata karya kwana, ta juya tana kara kallon tiredar.
Yanzu ya fito daga cikin tiredar, yana tsaye daga waje. Sai dai kaifafan idanuwan nan nashi suna kanta kyam. Wata irin kunya da faduwar gaba suka rufeta, musamman dan guntun murmushin da taga yana yi mata. Tayi saurin yin kasa da kanta, wani dan karamin murmushi itama yana ziyartar bakinta, kafin ta juya da sauri ta karya kwanar.